in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa a kasar Afrika ta Kudu sun yi bikin murnar cika shekaru 67 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin
2016-09-26 10:42:05 cri
A jiya ne Sinawa da ke kasar Afrika ta Kudu suka shirya wani kasaitaccen biki domin murnar cika shekaru 67 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin.

A jawabinsa yayin bikin, jakadan kasar Sin dake kasar Afrika ta Kudu Tian Xuejun ya bayyan cewa, a watan Disamban shekarar bara ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kawo ziyarar aiki kasar Afrika ta Kudu tare da shugabantar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika a birnin Johannesburg tare da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma. A wannan shekara, za a fara aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli. Kasar Sin da kasar Afrika ta Kudu da kuma sauran kasashen Afrika sun hada gwiwa sosai wajen cimma matsaya daya kan yadda ya kamata a aiwatar da sakamakon, sa'an nan an samu sakamako masu armashi na a zo a gani, lamarin da ya sheda kyakkyawar makomar hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika.

A nasa bangaren kuma, magajin birnin Johannesburg ya jinjina sakamakon da kasar Sin ta samu bayan da ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, da kuma rawar da Sinawa ke takawa wajen neman samun bunkasuwar birnin. Bugu da kari ya kuma yi maraba da Sinawa da su kara zuba jari a birnin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China