in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kara kwana guda a tattaunawar da ake yi game da kogin Nilu
2015-12-29 09:44:41 cri

Ministocin harkokin waje da na albarkatun ruwa na kasashen Sudan da Masar da Habasha su yanke shawarar kara kwana guda a tattaunawar da suke yi a birnin Khartoum game da shirin kasar Habasha na gina madatsar ruwa a kogin Nilu(GERD).

Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ibrahim Ghandour ne ya bayyana hakan a lokacin da yake yi wa taron labarai karin haske a karshen ganawarsu a jiya Litinin. Ya ce, yanzu haka sun cimma yarjejeniya a wasu fannoni. Suna kuma fatan cimma wata cikakkiyar yarjejeniya a karshen ganawar a yau Talata.

Manufar taron ministocin dai ita ce, cimma fahimtar juna game da shirin kasar Habasha na gina madatsar ruwa ta ruwan dake malala daga kogin Nilun da ya ratsa ta cikin kasashen uku.

A watan Maris din da ya gabata ne kasashen uku suka sanya hannu kan wasu yarjejeniya a birnin Khartoum na kasar Sudan, inda suka amince su ci gaba da tattaunawa kan yadda za a nazarci wannan batu da kuma yadda kasashen za su ci gajiyar ruwan da ke malala ta kogin na Nilu.

Shirin kasar ta Habasha game da gina wannan madatsar ruwa dai bai yi wa kasar Masar dadi ba, duk da shawarar da kwararrun al'ummomin kasashen uku suka gabatar a watan Satumban shekarar 2014, na ganin an gudanar da bincike game da tsarin shirin cin gajiyar ruwan da kuma tasirin hakan a bangaren muhalli, tattalin arziki har ma da rayuwar al'ummomin kasashen Sudan da Masar.

Kasar Habasha dai ta hakikance cewa, shirin zai taimaka mata wajen inganta tattalin arzikin kasar, musamman bangaren samar da hasken wutar lantarki.

Bayanai na nuna cewa, shirin da ake fatan kammala shi cikin shekaru uku, zai lashe kudin da ya kai dala biliyan 4.7. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China