in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga mata da su shiga a dama da su a yaki da cin hanci a nahiyar
2018-01-18 09:40:32 cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi kira ga daukacin matan Afirka da su shiga a dama da su a yakin da ake yi da matsalar cin hanci da rashawa a nahiyar. Wannan kira na zuwa ne yayin taron share fagen kungiyar AU karo 10 game da jinsi da aka bude a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Abban kasar Habasha.

A jawabinta na bude taro, kwamishinar kungiyar AU mai kula da harkokin siyasa Minata samate Cessouma, ta ce tarukan kolin share fage game da harkokin jinsi da aka gudanar a baya sun taka muhimmiyar rawa wajen karfafa da kuma daidaita manufofin kungiyar game da samar da daidaiton jinsi da samarwa mata abin dogora da kai.

Jami'ar ta ce, wannan taro wata dama ce ta nuna irin ci gaban da aka samu cikin shekaru goman da suka gabata, da kuma matakan da za a tsara a nan gaba, musamman a bangaren sabbin gyare-gyaren da aka yiwa kungiyar da ajadar raya nahiyar nan da shekarar 2063.

Ta kuma nanata cewa, cin hanci shi ne babbar matsalar dake hana aiwatar da manufofin raya nahiyar nan da shekarar 2063, ta ce irin wadannan dandali za su taimaka wajen inganta matakan kungiyar na yaki da cin hanci da rashawa.

Darektar kula da harkokin mata, jinsi da ci gaba ta kungiyar AU Mahawa Kaba Wheeler, ta ce makomar nahiyar ta dogara ne ga irin damammakin da aka tanadarwa matan da matasan nahiyar. Taken taron da za a kammala a gobe, shi ne "Yaki da matsalar cin hanci: Kyakkyawar hanyar samar da daidaiton jinsi da samarwa matan Afirka abin dogara da kai."(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China