in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron AU-EU: An yi kira da a zuba jari a fannin matasa
2017-11-30 09:11:21 cri

An bude taro karo na 5 na kasashen kungiyar hadin kan Afirka ta AU da takwararta ta tarayyar Turai EU a birnin Abidjan, birnin kasuwancin kasar Cote d'Ivoire, taron da aka yiwa take da "zuba jari a rayuwar matasa domin samar da makoma ta gari".

Jagorori daga nahiyar Turai da Afirka da dama ne suka halarci bude taron a jiya Laraba. Cikin manyan bakin hadda shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban Afirka ta kudu Jacob Zuma.

Taron na zuwa ne a gabar da kasashen Afirka ke kokarin dakile kalubalen rashin ayyukan yi tsakanin matasa, yayin da a nata bangare tarayyar Turai, ke fatan kawo karshen yawan aukuwar hare haren ta'addanci, da kuma kwararar bakin haure masu shiga Turai ba bisa ka'ida ba.

Yayin taron dai ana sa ran tattauna batutuwa masu nasaba da zakulo hanyoyin samar da guraben ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka. Kaza lika tarayyar Turai na fatan matasan Afirka, za su samu guraben ayyukan yi a kasashen su na asali.

A daya hannun kuma taron na yini biyu, zai tattauna game da batun inganta tsaro da wanzar da zaman lafiya, da kyautata ayyukan gwamnati, da zuba jari, da bunkasa harkokin cinikayya. Baya ga batun samar da ayyukan yi da na nishadantarwa.

Bayanai da aka gabatar yayin bikin bude taron dai sun mai da hankali ne matuka ga fannin kare kan iyakokin kasashe da kuma tsaro. Shugabanni na ta karfafa batun samar da damammaki na ayyukan yi ga matasan Afirka, tare da karawa kasashen nahiyar tallafin kudade domin yaki da kungiyoyin ta'addanci.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China