in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira ga 'yan sandan Sin da su kara daura damarar yakar masu zamba ta Intanet
2017-11-08 09:27:37 cri

Ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ta bukaci 'yan sandan kasar, da su kara daura damarar yakar masu zamba ta Intanet, musamman masu neman taimakon kudi ta hanyar da ba ta dace ba, hada-hadar kudi ta Intanet da makomar kasuwannin hannayen jari.

Wata takardar bayanai da ma'aikatar ta fitar na cewa, kasar Sin tana fama da masu almundahanan kudi dake shafar mutane da dama, lamarin da zama babbar barazana ga harkokin kudin kasar. Tana mai cewa, tilas a zage damtse wajen yakar wannan lamari.

Don haka, ma'aikatar ta yi kira ga 'yan sanda, da su sanya ido kan abubuwan da za su iya kawo illa ga harkokin kudin kasar, kana su inganta matakan gargadi da yin riga kafi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China