in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tanzaniya ta bayyana nasarorin da Magufuli ya cimma cikin shekaru 2
2017-11-06 09:46:59 cri

A ranar Lahadi gwamnatin Tanzaniya ta bayyana dunbun nasarorin da shugaban kasar John Magufuli ya cimma cikin shekaru biyu da suka gabata. Magufuli ya dare karagar mulkin kasar ne a ranar 5 ga watan Nuwambar shekarar 2015.

Darakta janar na sashen hukumar watsa labarai ta kasar Hassan Abbas ya bayyana cewa, daya daga cikin muhimman nasarorin da shugaban kasar ya samu shi ne maido da da'a a tsarin aikin gwamnatin kasar wanda hakan ya haifar da ingantuwar al'amurra a sha'anin aikin gwamnati.

Abbas ya bayyana cikin wani shirin gidan talabijin na kasar Tanzaniya cewa, an samu babbar nasara wajen takaita kashe kudaden gwamnati da kuma yin taka-tsan-tsan wajen kashe kudade a ayyukan da gwamnatin ke gudanarwa.

Ya ce, gwamnatin kasar ta gano ma'aikatan bogi sama da 30,000 da wasu ma'aikatan wadanda ke da takardun bogi, lamarin da ya sanya kasar ta samu rarar kudi kimanin dala miliyan 190 na kudaden albashin ma'aikata.

Babban mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana cewa, a kokarin yakin da gwamnatin Magufuli ke yi da rashawa, gwamnatin ta kafa wata kotun musamman, ta kuma sallami wasu jami'an gwamnatin masu yawa wadanda aka samu da hannu dumu dumu wajen aikata rashawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China