in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahara 2 a Califonia na dauke da muggan makamai, in ji jami'an 'yan sandan Amurka
2015-12-04 10:37:57 cri

Jami'an 'yan sandan Amurka sun fada a ranar Alhamis din nan cewar, mutanen nan 2 da ake zargi da bude wuta kan jama'a a ranar Larabar a birnin San Bernardino dake kudancin jihar Califonia ta kasar Amurka, suna dauke da muggan makamai.

Babban jami'in hukumar 'yan sanda na birnin San Bernardino Jarrod Burguan, ya fada a taron manema labarai cewar, mutane 14 ne suka mutu, yayin da wasu 21 suka jikkata a yayin wannan mummunan al'amari.

Burguan, ya ce, maharan biyu miji da mata ne, wato 'dan asalin kasar Amurka Syed Farook mai shekaru 28, da matarsa Tashfeen Malik mai shekaru 27.

Jami'in 'yan sanda ya kara da cewar, an samu wasu bututu kimanin 12 makare da bam, da kuma wasu kayayyakin hada boma bomai a gidan da suke haya cikin sa, kuma an yi musayar wuta sosai tsakanin su da jami'an 'yan sanda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China