in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Spaniya ya yi watsi da Gwamnatin Cataloniya, yana mai kira da a gudanar da sabon zabe
2017-10-28 13:55:26 cri

Firaministan Spaniya Mariano Rajoy, ya sanar da korar shugaban Cataloniya Carles Puigdemont tare da watsi da Gwamnatinsa, yana mai kiran sabon zabe a yankin a ranar 21 ga watan Disamba.

Wannan ya biyo bayan matakin da majalisar dokokin yankin Cataloniyar ta dauka a jiya, na ayyana 'yancin kan yankin dake arewa maso gabashin Spaniya.

Mariano Rajoy, ya sanar da matakan ne bayan wani taron musamman na jami'an gwamnatinsa da aka yi a gidansa, domin yanke shawara game da yadda za a yi amfani da ayar doka ta 155 na kundin tsarin mulkin kasar.

Baya ga korar Puigdemont da gwamnatinsa, Firaministan ya kuma sanar da korar shugaban 'yan sandan yankin da rufe dukkan ofisoshin jakadancin yanki dake kasashen waje tare da korar wakilan gwamnatin yankin Cataloniya a Madrid da Brussels.

A jiya da yamma ne majalisar dattawan Spaniya ta amince da amfani da ayar doka ta 155 na kundin tsarin mulkin kasar, wadda ta soke 'yancin kan yankin Cataloniya tare da mika ragamar muhimman hukumominsa ga gwamnatin Madrid.

Kafin wannan a zauren majalisar dattawan, Mariano Rajoy ya bayyana sanar da 'yancin kan yankin a matsayin laifi.

Wasu majiyoyi daga gwamnatin sun bayyana cewa, gwamnatin ta Spaniya za ta daukaka kara a kotun kundin tsarin kasar game da ayyana 'yancin yankin.

Bugu da kari a ranar Litinin ne babban mai shigar da kara na gwamnatin zai gabatar da zargin 'tawaye' a kan shugaban Cataloniya Puidgemont da sauran mambobin gwamnatinsa, laifin da hukuncinsa ka iya zama zaman gidan yari na tsakanin shekaru 15 zuwa 30. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China