Jawabin sarkin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar, yaje-yajen aiki da kuma bore a yankin Catalan, inda bayanan 'yan sanda ke cewa, mutane kimanin 300,000 sun bazama kan tituna don nuna rashin amincewarsu da matakan da 'yan sandan Sifaniya da dogarai masu tsaron jama'a suka dauka yayin kuri'ar raba gardamar ta ranar Lahadi.
Sarki Felipe ya dora alhakin tashin hankalin kan mahukuntan yankin na Catalan, yana mai nanata cewa, matakinsu na neman 'yancin kan yankin ya sabawa kundin tsarin mulki.
Ya ce, halayyar mahunkuntan yankin na rashin hankali, ta sanya tattalin arzikin Catalonia da ma Sifaniya baki cikin halin rashi tabbas. A saboda haka ya ce, a wannan hali da ake ciki, hakkin mahukuntan kasar ne su tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Ibrahim)