in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Sifaniya na hadin gwiwar mutunta juna
2017-10-12 20:11:02 cri

Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan matakin da kasar Sifaniya ke dauka na kare hadin kasa, kabilu gami da yankunanta.

Madam Hua wadda ta bayyana hakan yayin taron maname labarai a nan birnin Brjing, fadar mulkin kasar Sin, ta ce kasashen Sin da Sifaniya kawayen juna ne, kuma za su ci gaba da bunkasa akalar dake tsakaninsu, ta hanyar mutunta muradu da 'yancin kasashen juna, da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna.

A ranar Talata ne dai, jagoran yankin Catalan dake arewa maso gabashin kasar Sifaniya Carles Puigdemont ya sanar da cewa, yankin ya yi nasara a kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a ranar 1 ga watan Oktoba. Ko da yake ya ce za a dakatar da ayyana 'yancin kan yankin, domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin Sifaniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China