in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi Allah wadai da harin Barcelona
2017-08-21 13:38:58 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta yi Allah wadai da harin birnin Barcelona na kasar Sifaniya wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da raunata jama'a.

Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi, shugaban hukumar zartaswa ta AU, Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin ta'addancin da aka kaddamar a yankin Las Ramblas na birnin Barcelona, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, wasu gommai kuma suka jikkata.

Faki, ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka a harin.

Kana ya nuna goyon bayan kungiyar AU ga gwamnati da al'ummar kasar Sifaniya da gwamnatin kasar.

Ya kara da cewa, harin ya sake nuna babbar barazana da 'yan ta'adda ke haifarwa ga dukkan yankuna da kasashen duniya baki daya, don haka ya bukaci kasa da kasa da su kara azama wajen yakar ta'addanci da dakile tsattsauran ra'ayi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China