Da yake jawabi ga taron, ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour, ya ce manufar taron ita ce, tattaunawa da amincewa da ingantattun hanyoyi da dabarun da za su samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba ga al'ummomi da kasashen dake yankin kahon Afrika.
Ya ba da misali da kalubalen da yankin ke fuskanta da suka hada da yakin basasa da rikice-rikicen siyasa da barkewar annobar cututtuka da rashin kyakkyawan tsarin kasa da bullowar kungiyoyin masu kaifin ra'ayin addini da kuma gasar kasa da kasa kan albarkatu.
A nasa bangaren, shugaban kwamitin aiwatar da manufofi na Tarayya Afrika Thabo Mbeki, ya jadadda muhimmancin warware batutuwan dake ci wa yankin kahon Afrika tuwo a kwarya. (Fa'iza Mustapha)