Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 68 da suka gabata, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, al'ummomin kabilu daban-daban sun zama tsintsiya madaurinki daya domin yin aiki tukuru, wajen gina kasa da yin kwaskwarima a gida. A bana, gwamnatin kasar Sin dake karkashin shugabancin Xi Jinping, ta nuna himma da kwazo wajen habaka tattalin arzikin kasa, da kara samar da guraben ayyukan yi ga jama'a a birane da garuruwa, da kyautata zaman rayuwar al'umma, da kuma kara kawar da kangin talauci da wasu mutanen kasar ke fama da shi. Har wa yau, gwamnatin kasar Sin ta gaggauta kawo sauye-sauye ga tsarin tattalin arzikin kasar, da inganta ayyukan kirkire-kirkire, gami da sanya sabon kuzari da karfi wajen fadada tattalin arzikin kasar da kyautata zaman rayuwar al'umma.(Murtala Zhang)