in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana bikin cika shekaru 68 da kafuwa
2017-10-01 12:20:18 cri

Da safiyar wannan rana sama da mutane dubu 115 da suka zo daga sassa daban daban na kasar Sin ne suka yi dandanzo a katafaren babban filin Tian'anmen dake birnin Beijing hedkwatar mulkin kasar, domin kallon bikin daga turar kasar a matsayin wani bangare na bikin murnar cika shekaru 68 da kafa jamhuriyar jama'ar Sin.

Tun da misalin karfe 6:05 na safiya yau Lahadi ne, dakarun tsaron kasar Sin suka yiwa tutar kasar rakiya zuwa dandalin na Tian'anmen. Dubun dubatar Sinawa da suka taru a dandalin sun yi shiru a lokacin da ake nuna taken kasar, kana an daga babbar tutar kasar sama.

Kallon yadda ake daga tutar kasar Sin sama a filin na Tian'anmen a ranar kafuwar kasar, ya kasance wani muhimmin bangare na bikin murnar ranar. Wasu da dama sun halarci bikin ne domin kashe kwarkwatar idonsu, yayin da wasu kuma ke halartar wajen taron domin nuna kishin kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China