in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar AU ta bukaci sassa daban daban su taimakawa Saliyo bisa bala'in da ya auka mata
2017-08-15 19:47:25 cri

Kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta bukaci kasashen Afirka da sauran abokan huldar ta na ketaren nahiyar, da su taimakawa kasar Saliyo, bisa bala'in zabtarewar laka, da ambaliyar ruwa da suka sabbaba hallakar 'yan kasar da dama.

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar ta AU Moussa Faki Mahamat, shi ne ya yi wannan kira, yana mai cewa akwai bukatar 'yan Afirka mazauna kasashen ketare, da dukkanin masu ruwa da tsaki su tallafi Saliyo, ganin yadda ta tsinci kan ta cikin wannnan mawuyacin hali, shekaru 2 kacal bayan fitar ta daga annobar cutar Ebola mai saurin kisa, wadda ta yi awon gaba da dubbin rayukan 'yan kasar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China