A cewar rahoton na GSMA, wannan zai zamo ci gaba mafi sauri da za a samu a wannan fanni a dukkanin fadin duniya, a hannu guda kuma hakan zai samar da karin GDPn kasashen yankin ta wannan bangare, tare da fadada samar da guraben ayyukan yi, da bunkasa kirkire-kirkire, da ma ci gaban zamantakewar al'ummar yankin.
Da yake karin haske game da hakan, babban daraktan kungiyar Mats Granryd, ya ce yankin na kudu da hamadar Sahara zai zamo kan gaba, a bangaren bunkasar hidimomin salula cikin shekaru masu zuwa, ta yadda al'ummun sa da dama, wadanda a baya ba su da ikon cudanya da juna, nan gaba za samu damar hakan.
Ya ce fannin hidimar layukan salula, zai bude karin damammaki na magance kalulaben da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya, da ilimi, da samar da makamashin lantarki, da tsaftacaccen ruwan da sauran muhimman sassa na ci gaba. (Saminu)