in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Adadin masu ta'ammali da wayar hannu a Afrika zai zarce biliyan guda
2016-11-15 11:20:54 cri
Wani kamfani mai suna Ovum dake London, yayi hasashen yawan mutanen dake amfani da layukan wayar hannu zai zarce biliyan daya kafin nan da watanni ukun karshe na shekarar 2016, inda ake saran adadin zai karu zuwa biliyan 1.02 nan da karshen wannan shekara.

Kamfanin na Ovum, ya bayyana hasashen ne cikin wani rahoton da ya fitar a Nairobin kasar Kenya a jiya Litinin, rahoton ya ce, zuwa karshen shekarar 2021 adadin mutanen dake ta'ammali da wayar hannu a nahiyar Afrika zai karu zuwa biliyan 1 da miliyan 330.

Matthew Reed, shine shugaban kamfanin Ovum mai kula da yankin gabas ta tsakiya da kuma Afrika, yace "a yayin da masu mu'amala da layukan wayoyin hannu a Afrika ya kai biliyan guda, a bayyane take karara cewa, matakai na gaba da za'a dauka shine bunkasuwar manyan na'urorin samar da fasahar da ake amfani dasu ga masu ta'ammali da layukan wayoyin hannu, da kuma samun kudaden shiga ta hanyar amfani da fasahohin na'urorin sadarwa irinsu kafafen yada labarai na zamani da yadda ake amfani da wayar hannu wajen tafiyar da al'amurran kudade".

Sai dai Reed ya kara da cewa, nahiyar ta Afrika ta kasance mafi koma baya, idan aka kwatanta da akasarin shiyyoyi na duniya wajen bunkasuwar manyan na'urorin samar da fasahar sadarwa, ya kara da cewa, akwai bukatar a kara inganta hanyoyin sadarwa a nahiyar domin samun babbar moriyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China