in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gadoji na kyautata rayuwar jama'ar kasar Sin
2017-06-16 12:00:01 cri

A baya bayan nan, ana gina sabbin gadoji kimanin dubu 10 a kowace shekara a nan kasar Sin. Yawan wadannan gadoji ya kai matsayin koli a duk fadin duniya. Birane da kauyuka da wadannan gadoji suke hadawa suna samun kyautatuwa matuka. 

Babbar gadar Gangzhuao da ta hada da biranen Hongkong da Macao, da kuma Zhuhai na lardin Guangdong dake nan kasar Sin, gada ce da ta zama mafi tsawo a duniya baki daya, wadda kuma ta ratsa yankin teku. Tsayinta ya kai sama da kilomita 50. An kuma yi hasashen cewa, za a fara aiki da ita a karshen shekarar nan ta bana. Idan aka bude ta kuma, lokacin da ake bukata wajen sufuri ta mota tsakanin Hongkong zuwa Zhuhai zai kasance rabin sa'a kacal.

Lin Qibin, jami'i mai kulawa da aikin hade sassan kamfanoni da mallakar su a wani ofishin lauyoyi dake Hongkong, ya kan yi zirga zirga tsakanin yankin Hongkong da sauran biranen kasar Sin. Yana kuma sanya ran cewa, gadar Gangzhuao za ta fara aiki cikin gaggawa. Lin ya ce,

"Idan zan je birnin Zhongshan, sai na yi shiri na musamman. Idan zan bi jirgin ruwa, dole ne na duba jadawalinsa. Idan zan tafi ta mota, zan shafe awoyi uku zuwa hudu idan babu cunkoson motoci. Yanzu idan zan yi aiki a Zhongshan ko Zhuhai, ba zan iya farawa yau ba sai dai gobe. A sabili da haka, muna matukar sanya ran cewa, wannan gada ta Gangzhuao, za ta ba da taimako sosai, musamman ma a fannin cinikayya."

Ya zuwa yanzu, ana yin nazari kan shirin raya biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Zhuhai, da Foshan, da Huizhou, da Dongguan, da Jiangmen, da Zhaoqing, da kuma yankunan musamman na Hongkong da Macao tare. Wasu manazarta sun bayyana cewa, wadannan birane da yankuna za su zama babban jigo na kyautata manufar bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a gida ta Sin. Lin Qibin yana ganin cewa, gadar Gangzhuao za ta taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da wannan shiri, shi ma zai ci gajiyarta. Ya ce,

"Gadar Gangzhuao wani babban aiki ne da ake gudanarwa. Kasar Sin tana kokarin hada birane guri daya domin samun ci gaba tare. Yanzu ana kokarin raya biranen Guangzhou, da Shenzhen, da Zhuhai, da Foshan, da Huizhou, da Dongguan, da Jiangmen, da Zhaoqing, da kuma yankunan musamman na Hongkong da Macao wuri daya, ba shakka za su samu karin ci gaba."

Kamar yadda babbar gadar Gangzhuao take, jama'a na matukar sanya ran amfana sosai daga babbar gadar Hangzhouwan da za ta ratsa yankin teku, da babbar gadar Beipanjiang da dai sauransu. Kuma hakika wannan buri na su ya cika.

Tsayin babbar gadar Hangzhouwan ya kai kilomita 36, wadda ta tashi daga gundumar Haiyan ta birnin Jiaxing na lardin Zhejiang a arewa, zuwa birnin Cixi na Ningbo a kudu. Qian Weixiang, manomi ne dake shuka ganyayen shayi a kauyen Longjing na yankin Xihu dake birnin Hangzhou dake lardin Zhejiang, ya kuma bayyana cewa, gadar Hangzhouwan baya ga rage bata lokaci da za ta yi, za kuma ta rage musu kashe kudi. Ya ce,

"Daga birnin Cixi na Ningbo zuwa gundumar Haiyan ta Jiaxing, tsayinsa na tafiyar ya kai kilomita 150. Dole ne sai an tashi daga Cixi a tafi zuwa birnin Hangzhou tukuna, daga bisani a isa gundumar Haiyan. Amma yanzu ba haka abun zai kasance ba. Ana iya bi ta gadar Hangzhouwan kai tsayi, inda tazarar hanyar tsakanin wuraren biyu za ta ragu zuwa kilomita 80, yayin da tsawon lokacin tafiyar ya ragu zuwa mintuna 80, yayin da kuma za a samu ragin kudin da ake kashewa na sufuri tsakanin sassan biyu zuwa kusan Yuan 50."

Babbar gadar Hangzhouwan ta rage tazarar hanyar dake tsakanin birnin Ningbo da Jiaxing, haka ma hanyar dake tsakanin Ningbo da Shanghai. Ta rage tazarar hanyar dake tsakaninsu sama da kilomita 100 a kasa. Cikin awoyi biyu kacal ana iya isa wurin da aka nufa.

Ban da haka, babbar gadar Beipanjiang da aka fara amfani da ita a bara, ita ma ta girgiza duniya baki daya. Wannan gadar da ta hada birnin Xuanwei na lardin Yunnan da gundumar Shuicheng ta birnin Liupanshui na lardin Guizhou, gada ce mai matukar tsayi a duniya. Tsayinta daga kasa zuwa sama ya kai mita 565, kamar dai tsayin wani babban gini mai hawa 200. Wannan gada ta kyautata yanayin da ake ciki a fannin sufuri a lardunan Yunnan da Guizhou da Sichuan da birnin Chongqing da sauransu, tare da sa kaimi ga raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummarsu yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China