170615-kasar-sin-a-idon-wani-dan-jaridar-zimbabuwe-lubabatu.m4a
|
A watan Maris na bara, Lovemore Chikova ya zo kasar Sin a karo na shida, inda ya shafe tsawon watanni goma yana halartar wani kwas na cibiyar musayar ra'ayoyi tsakanin manema labarai na Sin da Afirka da kasar Sin ta shirya. Ban da horaswa, ya kuma ziyarci wurare da dama na kasar Sin tare da takwarorinsa na kasashen Afirka, inda ya gane ma idonsa bunkasuwar kasar. Kimanin rabin shekara ne da Mr. Chikova ya koma kasarsa daga kasar Sin, amma har yanzu ya kan ce ya bude ido idan aka tambaye shi yaya kasar Sin ta burge shi. A ofishinsa, ya ajiye wani samfuri na jirgin kasa mai saurin tafiya na kasar Sin, tare kuma da wani littafi game da yadda kasar Sin ke saukaka fatara a gefe. A cikin jakarsa kuma, akwai wani littafi da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken "fid da kai daga kangin talauci". Ya ce, "Kasar Sin ta cancanci yabo. Kasar Sin ta yi gyaran fuska sosai, idan na kwatanta yadda take a yanzu da kuma yadda na ganta lokacin da na ziyarci kasar a shekaru 10 da suka wuce. A ganina, akwai sauye-sauye a kasar a kowace shekara."
A ziyararsa kasar Sin a shekarar bara, Mr. Chikova ya shiga jirgin kasa na zamani mai saurin tafiya na kasar Sin, kuma ya ga motocin da ke amfani da sabbin makamashi da ma jirgin sama maras matuki na kasar, ya kuma je larduna sama da 10 na kasar. Duk da haka, abin da ya fi burge shi shi ne yadda al'ummar kasar ke hada karfi su zama tsintsiya madaurinki guda a wajen bunkasa kasarsu. Ya ce, "Al'ummar kasar Sin suna da buri na bai daya na samun ci gaban kasarsu, kuma yadda suke hada karfi da karfe wajen cimma burin ya burge ni sosai. Kusan duk in da na shiga, ana tattaunawa kan yadda za a bunkasa kasar."
Kullum Mr. Chikova na tunanin ta yaya kasar Sin ta zama ta biyu a duniya ta fannin ci gaban tattalin arziki, kuma mene ne Zimbabuwe ke iya koya daga kasar Sin? A tsawon watanni goma da yake halartar kwas din, ya samu amsa ga tambayarsa, ya ce, "Na farko shi ne hada kai, wato a hada kai tsakanin gwamnati da al'umma. Maganar ci gaban kasa za ta zama maras ma'ana idan ba a samu sa hannun al'umma ba. Na biyu shi ne a mai da hankali kan tabbatar da manufofin da aka tsara. A kasar Zimbabuwe, ana tsara manufofin bunkasa tattalin arziki da yawa a kowace shekara, sai dai kalilan ne ake iya aiwatar da su. Amma a kasar Sin, idan an kaddamar da wani shiri ko wata manufa, lallai za a aiwatar da ita. Misali ana shirin gina wani babban gini a birnin Beijing, za ka ga an tsara wani jadawali na gina ginin, sa'an nan a gudanar da aiki mataki da mataki bisa ga jadawalin. Wadannan su ne abubuwa da ya kamata mu koya daga kasar Sin."
Daga watan Afrilu na shekarar 2016, Mr. Chikova ya bude wani bangare mai taken "Mu leka Sin da Afirka" a jaridar nan ta Herald, inda yake bayani a kan ci gaban kasar Sin. Har zuwa yanzu kuma, yana rika bayar da bayani sau daya a kowane mako, ya ce, "Na shafe watanni sama da 10 ina kasar Sin, amma idan ban gabatar da abubuwan da na koya a kasar Sin da kuma fadakar da gwamnatinmu, da al'ummarmu, a kan ci gaban kasar Sin da kuma abubuwan da muke iya koya daga kasar ba, lalle, ziyarata za ta zama maras amfani." (Lubabatu)