in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kaddamar da layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi sakamako ne na hadin kan da Sin da Kenya suka samu
2017-06-01 19:46:17 cri

Yau Alhamis 1 ga watan Yuni, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyama a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing cewa, layin dogo tsakanin biranen Mombasa da Nairobi na kasar Kenya wato SGR a takaice da aka kaddamar, sakamako ne da kasashen Sin da Kenya suka samu wajen inganta zumuncinsu da yin hadin gwiwar moriyar juna. Har ila yau yayin da take amsa tambayar manema labaru dangane da damuwa kan gazawar gwamnatin Kenya wajen biyan rance mai ruwa, madam Hua ta jaddada cewa, kasar Sin, aminiyar kasashen Afirka ce ta gaskiya a fannin samun ci gaba.

Ranar 31 ga watan Mayu ne manzon musamman na shugaban kasar Sin kuma mamban majalisar gudanarwar kasar ya halarci bikin kaddamar da layin dogo, inda ya yi murnar kaddamar da layin dogon a madadin shugaba Xi Jinping na kasar Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China