in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da layin dogon SGR a kasar Kenya
2017-05-31 17:45:35 cri

A yau ne Laraba, shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya kaddamar da layin dogon fasinja mai tsawon kilomita 480 daga Mombasa zuwa Nairobi, babban birnin kasar.

Da yake jawabin yayin bikin kaddamar da layin a hukumance, shugaba Kenyatta ya ce layin dogon ya bude wani sabon babi na tarihi a kasar, kana ya maye gurbin tsohon layin da aka gina tun zamanin Turawan mulkin mallaka na kasar Burtnaiya shekaru sama da 100 da suka gabata.

Shugaban ya kuma bayyana gabanin kaddamar da layin dogon cewa, yana daya daga cikin muhimman nasarorin da kasar ta cimma a yunkurinta na farfado da masana'antu da makomar kasar dake samun matsakaicin kudaden shiga.

Ya kuma danganta nasarar kaddamar da layin dogon kan dangantakar dake tsakanin Sin da kasar Kenya.

Kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin ne ya gina layin dogon wanda ya lashe tsabar kudi dala biliyan 3.8, sai dai kaso 90 cikin 100 na aikin ya fito ne daga kasar Sin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v An kaddamar da layin dogon SGR a kasar Kenya 2017-05-31 17:45:35
v An fara aiki da hanyar dogo ta SGR 2017-05-31 16:24:36
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China