in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude taron WAGP a kasar Benin
2017-05-12 09:29:13 cri
A yau Jumma'a ne a birnin Cotonou na Jamhuriyar Benin ake saran bude wani taron shiyya game da hanyoyin kawar da abubuwan dake kawo nakasu game da aikin shimfida bututun iskar gas na kasashen yammacin Afirka(WAGP)

Wata sanarwa da aka fitar jiya Alhamis a hukumance a birnin Cotonou game da wannan aiki, ta bayyana cewa, kwamitin ministocin WAGP, da kwamishinonin kula da hakar ma'adinai da makamashi na kungiyar ECOWAS su ma za su gana game da wannan aiki.

Shi dai wannan aiki na shimfida bututun iskar gas a kasashen yammacin Afirka, wani shiri ne na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da sassan masu zaman kansu, wadanda suka hada da kasashen Benin, da Togo, da Ghana, da kuma Najeriya wadda ke kan gaba wajen samar da albarkatun iskar gas.

An dai tsara wannan aiki ne ta yadda al'ummomin da ke wadannan kasashe za su yi amfani da iskar da Najeriya ke samarwa wajen samar da isasshen hasken wutan lantarki mai inganci kuma cikin rahusa.

Aikin wanda aka kirkikro shi a shekarar 1995, ya fara samar da makashin iskar gas ga jama'a daga watan Maris na shekara 2011 amma daga bisani ya fuskanci wasu tarin kalubale.

Sai dai yadda tsagerun 'yan tawayen Niger Delta suke barnata bututun mai a Najeriya da matsalar kudi da ta addabi kamfanin samar da iskar gas na yammacin Afirka da tarin bashin ake bin hukumar kula da kogin Volta ta kasar Ghana, suna daga cikin abubuwan da suka rage bukatar iskar gas din.

Bayanai na nuna cewa, kamfanin Chevron-Texaco da Shell, da kamfanin samar da mai na Najeriya NNPC, da hukumar kula da kogin Volta ta kasar Ghana(VRA) su ne ke rike da kaso 96 cikin 100 na wannan aiki. Yayin da a hannu guda kuma kamfin BenGAZ SA na kasar Benin da SOTOGAZ na kasar Togo ko wanne ke rike da kaso 2 cikin 100.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China