in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sashen kirar jiragen sama na Sin na daf da shiga wani sabon matsayi
2015-03-11 09:35:27 cri

Nan ba da jimawa ba kasar Sin za ta kaddamar da sabon sanfurin jirgin sama na dakon kaya kirar gida mai lakabin Kunpeng Y-20. Jirgin da ake fatan fidda shi kasuwa zai zamo wani muhimmin mataki, na bunkasa fannin kira, da cinikayyar jiragen saman kasar.

A cewar Tang Changhong, wanda ke matsayin mataimakin babban injiniya a hukumar lura da harkokin sufurin sama na kasar Sin AVIC, tun cikin shekarar 2013 aka yi gwajin jirgin, bayan shafe shekaru 7 ana kirar sa.

Mr. Tang ya ce, jirgin wanda kamfanin kirar jiragen sama na birnin Xi'an ya samar na kunshe da sabbin fasahohin zamani, da za su ba shi damar jure dukkanin wani yanayi na sufuri da ake bukata. Zai kuma kasance muhimmin mataki na bunkasar sashen masana'antun kirar na'urorin zamani a kasar.

Ya ce, baya ga Kunpeng Y-20, Sin za ta fitar da wasu manyan jiragen dakon fasinjoji kirar C919 da kuma AG600. Kana ana fatan AG600 zai fara aikin jigilar fasinja cikin shekarar 2016 dake tafe. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China