in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Za a fara gudanar da bikin "Ranar tambarin kaya" na shekara shekara
2017-05-02 20:11:51 cri

Kwamitin zartaswar kasar Sin ya amince da kebe ranar 10 ga watan Mayu na ko wace shekara, a matsayin "Ranar tambarin kaya" da kamfanonin kasar Sin ke sarrafawa.

Wata sanarwa da aka fitar a Talatar nan ta nuna cewa, shawarar hakan ta biyo bayan bukatar da hukumar samar da ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar Sin NDRC ta mika ne ga kwamitin, ana kuma sa ran hukumar ta NDRC, da sauran wasu sassan gwamnati ne za su tsara ayyukan da za a rika gudanarwa a wannan rana.

Ana fatan amfani da wannan rana wajen fayyacewa duniya tambarin kayayyaki daban daban da kamfanonin kasar Sin ke samarwa, tare da karin haske game da irin nasarori da suka cimma a kasuwannin duniya.

Tun a bara ne dai kwamitin zartaswar kasar Sin ya gabatar da ka'idojin kafa wannan rana, wadda ake fatan za ta bada gudummawa, ga daidaita bukatun kasuwa yadda ya kamata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China