in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban WIPO ya yabawa ingancin tambarin kayayyakin Sin
2017-03-16 10:42:47 cri

Darakta janar na hukumar kare hakkin mallaka ta duniya Francis Gurry, ya yabawa kasar Sin game da kokarinta na kare ingancin tambarin kayayyaki na kasa da kasa.

Da yake ganawa da manema labarai a jiya, Francis Gurry ya ce, kokarin na kasar Sin ya fita daban, inda ya ce, ingancin kayayyakin kasar ya karu da kashi 44 cikin shekara guda.

Ya ce, ingancin tambarin kayayyakin da hukumar WIPO a biranen Madrid da Hague ke kula da su, ya nuna cewa, a cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ce ta zo na hudu ta fuskar ingancin tambarin kayayyaki da aka yi a shekarar 2016.

Kamfanonin dake neman rajista na kasar Sin sun taimaka wajen habaka ci gaban da aka samu ta fuskar kare tambarin kayayyaki, al'amarin dake fadada kasuwancin kasar zuwa wasu kasashen duniya a daidai lokacin da kasar ke canza hanyarta daga samar kayayyaki zuwa yadda kayayyakin ke fadada zuwa sauran sassan duniya. (Fa'iza Mutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China