in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban aikin masallacin Alger da wani kamfanin kasar Sin ke ginawa ya kammala da kashi 72 cikin 100
2015-09-20 13:42:28 cri
Ayyukan babban masallacin Alger, da kamfanin kasar Sin CSCEC ke ginawa, na gudana yadda ya kamata, kuma babban aiki ya kammala da kashi 3 cikin kashi hudu, in ji ministan gine gine da muhalli na kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune a ranar Asabar a yayin da ya kai wata ziyarar gani da ido a wurin da aikin ke gudana a karkarar dake gabashin babban birnin kasar.

Babban aiki ya kammala da kashi 72 cikin 100, in ji ministan, inda ya kara da cewa aikin yin ado a zauren sallah dake fadin murabu'in mita dubu 20 zai fara a cikin watan Febrairu mai zuwa.

A karshe za a mika wannan masallaci cikin wa'adin da aka tsaida, wato cikin watan Satumban shekarar 2016, a cewar ministan Aljeriyan.

An fara aikin gina wannan masallaci a ranar 28 ga watan Febrairun shekarar 2012 kuma ya kamata a kammala cikin shekaru uku da rabi, bisa kudin kwangilar da ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 1,098.

Bisa fadin murabi'in hekta 20, babban masallacin Alger zai iya karbar masulmai kusan dubu 120. Kuma ya kunshe dakuna daban daban guda goma sha biyu, da babban zauren sallah, wani dandamali da tsaunin masallaci na mita 270. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China