in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar kyanda ta barke a Guinea
2017-02-12 12:50:27 cri
Wata majiya daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Guinea ta ce, zuwa shekaranjiya wato 10 ga wata, akwai mutane 417 wadanda ake zargin sun kamu da cutar kyanda, ciki har da mutane 122, wadanda aka riga aka tabbatar da cewa, sun kamu da cutar. Kawo yanzu babu wanda ya mutu a cikinsu.

A nasa bangaren, ministan kula da harkokin kiwon lafiya na Guinea Abdourahmane Diallo ya yi kira ga iyaye maza da mata, da su yiwa yaransu allurar rigakafi. Kana ministan ya ce, idan iyaye sun gano yaransu suna da alamu na mura, dole ne a garzaya da su asibiti don samun jinya ba tare da bata lokaci ba.

Wakilin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO dake kasar Guinea ya bayyana cewa, WHO za ta hada kai da ma'aikatar kiwon lafiya ta Guinea, a kokarin sa'ido don taka birki ga yaduwar cutar kyandar, da kuma kulawa ga wadanda suka kamu da cutar yadda ya kamata.

Haka zalika, wakilin WHO ya nemi a kara adadin yaran da za'a ba su allurar rigakafin, ta yadda za'a taimaka sosai ga shawo kan yaduwar cutar.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China