in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Guinea za ta yi hadin gwiwa da Sin a dukkan fannoni
2016-10-26 10:30:12 cri

Kafin ziyarar kwanaki 10 da zai yi a kasar Sin, shugaban kasar Guinea Alpha Conde, ya bayyana a yayin da yake ganawa da manema labaru a fadarsa cewa, cigaba da karfafa hadin gwiwa tare da Sin a fannin tattalin arziki na da muhimmanci sosai, kasar Guinea tana fatan za ta yi hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin samar da muhimman ayyukan more rayuwa, da zamanintar da aikin gona, da kuma raya kimiyya da fasaha.

An ba da labari cewa, a lokacin ziyarar ta Mista Conde, kasashen biyu za su yi musayar ra'ayi kan huldar dake tsakaninsu, da kuma batutuwan da suka dora muhimmanci a kai. Ban da birnin Beijing, Alpha Conde zai kai ziyara a lardunan Shaanxi da Sichuan, kana zai halarci bikin baje koli na kasa da kasa a yammacin kasar Sin karo na 16. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China