in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar yin gyare-gyare kan aikin gona domin habaka lalitar manoma
2017-02-07 10:53:16 cri

A ranar Lahadin karshen makon jiya ne kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwa, wato gwamnatin kasar, suka fitar da wata takarda mai lamba 1 ta shekarar 2017, wanda ke kunshe da shirin su na ci gaba da mai da hankula ga batun bunkasa yankunan karkara na kasar Sin.

A cikin wannan takarda, an nanata cewa, dole ne a zurfafa aikin yin gyare-gyare kan aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa, ta yadda za a iya samun sabon karfin bunkasa yankunan karkara. Sabili da haka, a jiya Litinin, wani babban jami'in hukumar ba da jagoranci kan ayyukan yankunan karkara a kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya jaddada cewa, yunkurin cika jaka ko lalitar manoma, shi ne ma'aunin da zai tabbatar ko ana samun nasarar gyare-gyare a fannin aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa ko a'a.

A wani taron manema labaru da ofishin watsa labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya a jiya Litinin, direktan ofishin hukumar ba da jagoranci kan ayyukan yankunan karkara na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Mr. Tang Renjian ya nuna cewa, an dauki wannan mataki ne bisa hakikanin halin da ake ciki a yankunan karkara, da aikin gona na kasar Sin. Mr. Tang ya ce, "A halin da ake ciki yanzu haka, babbar matsalar da ake fuskanta game da aikin gona ba wai batun rashin samun isashen amfanin gona ba ce, wato matsala ce da ake da ita game da tsarin amfanin gona, wato a wasu lokuta, ana samar da kayayyakin amfanin gona fiye da bukatun da ake da su, yayin da a wasu lokuta, ba a iya samun isashen kayayyakin gona da ake bukata. Hanzarta yin gyare-gyare kan aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa, da kuma kokarin kyautata karfin takarar amfanin gona a kasuwa, domin kokarin kara moriyar aikin gona, wani muhimmin aiki ne da kasar Sin za ta yi a yanzu, da ma kuma a nan gaba a lokacin da take kokarin gyara, da kuma kyautata manufofin aikin gona. "

A hakika dai, batun yin gyare-gyare ga aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa, wani sabon tunani ne da ake da shi bisa halin da kasar Sin take ciki a fannin bunkasa aikin gona da yankunan karkara. Mr. Tang Renjian ya kara da cewa, idan an kwatanta manufofin daidaita tsarin aikin gona da aka gudanar a cikin shekaru da dama da suka gabata, za a gano cewa, wannan sabon tunani na yin gyare-gyare kan aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa yana da sabuwar ma'ana. Tang Renjian yana mai cewa, "Akwai bambanci a fannoni uku, wato, da farko dai, a da an fi mai da hankali kan yadda za a warware matsalar rashin samar da isassun kayayyakin amfanin gona da ake bukata, amma yanzu a lokacin da ake kokarin daidaita yawan kayayyakin amfanin gona iri iri, an fi mai da hankali wajen kyautata ingancin kayayyakin amfanin gona, da takararsu a kasuwa, domin kokarin samun dauwamammen karfin bunkasa aikin gona. Bugu da kari, a da, a kan mai da hankali kan tsarin aikin gona, amma yanzu za a fi mai da hankali kan tsarin ire-iren kayayyakin amfanin gona. Sannan, a da, an fi mai da hankali kan aikin gona kawai, amma yanzu an fi mai da hankali kan yadda za a gyara tsare-tsare, da kuma manufofin bunkasa aikin gona."

A 'yan shekarun nan, wasu manoma 'yan ci rani da suka koma garuruwansu sun bunkasa sana'o'in shan iska, ko yawon shakatawa a kauyuka, ko sayar da kayayyakin amfanin gona ta shafin Intanet. Wadannan sabbin sana'o'in da ake bunkasawa a kauyuka, suna kawo wa manoma arziki cikin sauri. Mr. Han Jun, mataimakin daraktan ofishin hukumar ba da jagoranci kan ayyukan yankunan karkara, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, gwamnati za ta goyi bayan manoma wadanda suke kokarin bunkasa yankunan karkara a fannonin samun izinin samun gonaki, da horar da ma'aikata, da sha'anin hada-hadar kudi. Mr. Han ya ce, "Alal misali, game da bukatar gonaki domin bunkasa sabbin sana'o'i a yankunan karkara, wannan takarda ta bayyana cewa, za a kyautata tsarin tabbatar da samar da sabbin gonaki domin neman bunkasuwa. A bana, za a kebe wasu gonaki domin goyon bayan sabbin sana'o'in da za a bunkasa a yankunan karkara. Bugu da kari, manoma za su iya samun sabbin filayen bunkasa sabbin sana'o'insu ta hanyar gyara kauyukan da suke da zama."

Wannan aiki na gyare-gyare kan aikin gona bisa bukatun da ake da su a kasuwa, aiki ne da za a yi cikin dogon lokaci mai zuwa. Gwamnatin kasar Sin ta kuma jaddada cewa, a lokacin da ake wannan aiki, ba za a iya rage yawan kayayyakin amfanin gona da ake samarwa ba, kuma ba za a rage yawan kudin shiga da manoma suke samu ba. Daga karshe kuma, dole ne a tabbatar da kwanciyar hankali a yankunan karkara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China