"A lokacin da, wannan wuri wani tsohon gini ne na duwatsu, wanda yake da yanayi na musamman na lardin Fujian sosai. Bayan da muka yi masa kwaskwarima, mun hada halin musamman na lardin da kuma yanayi irin na zamani. Alal misali, a bene na biyu, mun kiyaye beam da bulo na gargajiya, wadanda ba a iya kera su a zamanin yau. Game da sauran wurare, mun yi musu kwalliya irin ta zamani."
Yayin da take tabo managar, Hu Pan ta yi murmurshi, kuma ta gaya mana cewa, ita wata mutumiya ce da ko da yaushe take mai da hankali kan aikinta sosai. Don haka yadda za a iya hada al'adun gargajiya na Quanzhou dana zamanin yau yadda ya kamata wani batu ne da ta kan yi tunani a kai a koda yaushe.
Bayan da suka yi kwalliyar har na tsawon fiye da rabin shekara, a karshe dai an kaddamar da kantin sayar da kofi na Huayuanli a watan Mayu na shekarar 2016, wanda ya janyo hankalin masu yawon shakatawa da mazauna wurin sosai.
"A wasu lokuta, masu yawon shakatawa da ke titin na da dimbin yawa har ma ya wuce abin da ake zato. Wasu masu yawon bude ido kan je bene na uku na kantinmu don daukar hoton wata hasumiya. A waje daya kuma, kyaun kantinmu shi ma ya samar musu wani muhalli na daukar hotuna."
Amma a ganin mai kantin Jin Xu, duk wadannan abubuwa wani masomi ne kawai.
"Muddin aka ba ni wani dandali, to zan iya fitar da sabbin ra'ayoyi, kamar muna iya shirya wasu harkokin da kara fahimtar masu yawon shakatawa da mazauna wurin."
Birnin Quanzhou wani birni ne mai yawan al'adun gargajiya, kuma sakamakon dogon tarihinsa da kuma haduwar al'adun kasa da kasa da kuma addinai daban daban a matsayinsa na masomi na hanyar siliki na teku, birnin yana burge mutane sosai. Kamar yadda Hu Pan da Lin Xiaodong da kuma Jin Xu ke yin kokari a nan don cimma burinsu, a zamanin yau, Quanzhou zai iya samar da wani dandali ga kowane mutumin da ke da aniyar cimma burinsa bisa kokarin da yake da shi.
Da ganin yadda baki ke haduwa a cikin kantinsa, suna shan kofi, suna fahimtar tarihin Quanzhou, suna gano sabon karfin da birnin ya nuna, Jin Xu shi ma ya fara jin dadin da haduwar tarihi dana zamani da al'adun gargajiya da na zamani suka kawo masa.(Kande Gao)