161228-huayuanli-tm.mp4
|
Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu leka birnin Quanzhou dake lardin Fujian a kudancin kasar Sin, domin mu fahimci yadda wannan birni yake, shi dai birnin Quanzhou ya kasance mai matukar janyo hankulan jama'a daga sassa dabam dabam na duniya, sakamakon irin matsayin da wannan birni yake dashi ta fuskar abubuwan tarihi, a matsayinsa na yanki mai dadadden tarihi, birnin Quanzhou ya shahara matuka, kasancewarsa a nan tushen kafa harkokin cikin siliki na kan teku, shekaru sama da dubu da suka shude.
161226-Haduwa-a-kantin-sayar-da-kofi-na-Huayuanli-don-kara-fahimtar-birnin-Quanzhou-Kande.m4a
|
"Duk lokacin da na zo wurin, na kan shiga wannan kanti. A kwanakin baya na sayi wata riga a nan, kuma mai kantin ne ya yi zanin da kansa a jikinta."
Xiaozhang, wani bako ne mai sha'awar zane-zane wanda yakan je kantin sayar da kofi na "Huayuanli" kullum, wanda yake kan titin Xijie na birnin Quanzhou. Dalilin da ya sa kantin ya jawo hankalinsa sosai, sabo da wasu zane-zane da aka sanya a cikinsa, wadanda ba kasafai ake samun irinsu a sauran wurare ba. Xiaozhang ya gaya mana cewa, mai kantin Jin Xu shi ne ya tsara zane-zanen da kansa.
Jin Xu, wanda ya fara koyon fasahar zane-zane tun lokacin da yana karami, ma'aikaci ne a wani kamfani a Beijing. Kuma sabo da wani zarafi na aiki ya je birnin Quanzhou, lamarin da ya sa ya kafa gindin zama a wannan birnin dake da tarihi fiye da shekaru dubu daya.
"Quanzhou wani birni ne mai yawan al'adu, baya ga kasancewarsa mai dadadden tarihi na fiye da shekaru dubu daya, akwai kuma addinai daban daban a yankin."
A farkon shekarar 2015, Jinxun ya kafa wani dakin zane-zane a birnin Quanzhou. Ya gaya mana cewa, dalilin da ya sa ya yi haka shi ne sabo da al'adun da ake iya samu a birnin suna iya kawo masa sabbin abubuwan da ake ji a rai a ko wace rana, hakan ya sa ba ya so ya bar shi, a maimakon haka, ya kafa gindin zamansa a nan don kara fahimtar birnin.