A yayin taron musamman da hukumar ta gudanar a cibiyar MDD dake birnin New York a wannan rana, babban masani na hukumar mai kula da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa Wang Xiaojun ya bayyana cewa, bisa ga hadakar za a tattara muhimman bayanai da shawarwari daga masana daga kasashe masu tasowa da masu ci gaba a fannin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, kana za a tsara wasu manufofi da dokoki, ta yadda za a raya hadin gwiwa bisa doka da tsari.
Hadakar za ta kunshi sama da masana 200 daga sassa daban-daban na duniya . (Zainab)