in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sake kalubalantar bangarori daban daban da su dakatar da shirinsu na girke na'urorin THAAD
2016-11-16 19:26:44 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Laraba a nan birnin Beijing cewa, Sin ta sake kalubalantar bangarorin da abin ya shafa da su maida hankali ga damuwar kasar Sin tare da dakatar da shirinsu na jibge na'urorin kakkabo makamai masu linzami sanfurin THAAD.

Geng Shuang ya bayyana cewa, jibge wadannan na'urori da kasar Amurka ta ke shirin yi a kasar Koriya ta Kudu, zai kawo illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da moriyar kiyaye tsaro a kasashen dake yankin ciki har da kasar Sin. Kuma hakan zai dakile kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Koriya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China