Mr. Geng ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka yi a Juma'ar nan, inda ya ce Sin ta riga ta bayyana matsayinsa kan wannan batu sau da yawa. A cewarsa, girke na'urorin na THAAD a kasar Koriya ta Kudu da Amurka ke nufin aiwatarwa, ba zai kawar da damuwar bangarorin da batun ya shafa ba, kuma ba zai haifar da nasara ga cimma burin dakile makaman nukiliya a zirin Koriya ba. Kaza lika, ba zai wanzar da zaman lafiya a zirin ba.
Baya ga haka, matakin zai lahanta moriyar kasashen shiyyar ta fuskar tsaro, ciki har da kasar ta Sin, zai kuma wargaza daidaito a fannin manyan tsare-tsaren shiyyar. Don haka kasar Sin ke adawa matuka da wannan mataki. Za kuma ta dauki matakai da suka wajaba, domin kiyaye tsaronta, da kuma tabbatar da daidaiton shiyyar ta fannin manyan tsare-tsare. (Bilkisu)