A cikin sanarwar Ban ya ce, kasar Cote d'Ivoire ta zartas da sabon kundin tsarin mulkin kasar ne bayan jefa kuri'ar raba gardama a ranar 30 ga watan Oktoba. A cewarsa, wannan zai taimaka wajen sassauta yanayin da kasar ke ciki, da kawar da bambanci a tsakanin bangarori daban daban.
Baya ga haka, Ban ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar da su kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu ta hanyar da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, kana da gudanar da tattaunawa da nufin shirya zaben majalisar dokoki a makwanni masu zuwa yadda ya kamata. (Bilkisu)