in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kunshi mutane tsoffi da ba su iya dogaro da kansu miliyan 42 nan da shekarar 2020
2016-10-27 10:48:08 cri

Kasar Sin za ta kunshi miliyan 42 na mutane tsoffi da ba su iya dogaro da kansu nan da shekarar 2020, kana wannan adadi zai ninka sau biyu nan da shekarar 2050, a cewar wani jami'in kwamitin kasa dake aiki kan tsufa.

Sin ta sami babbar karuwar yawan mutane tsoffi da ba su iya kulawa da kansu, da suke rayuwa su kadai ko wadanda yawan shekarunsu na aifuwa ya zarce shekaru 80.

Wadannan gungun mutane dukkansu suna da wata bukatar gaggawa ta ayyukan ba da kulawa, in ji Li Zhihong, maitamakin shugaba na cibiyar bincike kan manufofin siyasa na kwamitin, a yayin wani dandali kan ba da kulawa ga mutane tsoffi da aka shirya a ranar Laraba a Tianjin, birnin bakin teku dake arewacin kasar Sin.

Kasar ta Sin za ta kunshi mutane tsoffi da ba su iya dogaro da kansu kusan miliyan 97.5 nan da shekarar 2050. Wannan adadi na mutane tsoffi masu fiye da shekaru 80 zai cimma miliyan 29 a shekarar 2020 da miliyan 108 a shekarar 2050.

Baya da haka, kasar za ta kuma kunshi mutane tsoffi miliyan 118 dake rayuwa su kadai ko wadanda 'yayansu ba su kula da su ba nan da shekarar 2020, kana miliyan 262 nan da shekarar 2050.

A cewar mista Li, tsufan al'umma zai wakiltar wasu manyan damammaki ga masu ba da kulawa ga mutane tsoffi a kasar Sin, kuma ana yawan amfani da fasahohin zamani a wannan fanni. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China