in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban Sin ya nuna juyayi kan rasuwar sarki Bhumibol Adulyadej
2016-10-23 13:05:41 cri
Jiya Asabar, manzon musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kuma mataimakin shugaban kasar Li Yuanchao ya tafi kasar Thailand, don nuna juyayi kan rasuwar sarkin kasar Bhumibol Adulyadej.

A yayin da yake ganawa da mataimakin firaministan kasar Thailand Narong Pipattanasai, mista Li ya bayyana cewa, kasarsa na mayar da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da Thailand, tana kuma kulawa da zumunta a tsakaninta da gidan sarautar Thailand, tana mai imanin cewa, ko shakka babu za a ci gaba da irin wannan dangantaka har abada. Kana Li ya kara da cewa, kasarsa na fatan yin kokari tare da Thailand, don yada zumunta, kara nuna amincewa ga juna da kuma karfafa hadin kai, da nufin kawo gajiya ga jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangaren, mista Narong ya bayyana cewa, masu jinin masarautar Thailand su kan kai ziyara a kasar Sin, za kuma su gaji ra'ayin sarkinsu, don ciyar da sha'anin sada zumunta a tsakanin kasashen biyu gaba. Narong ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasarsa na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da Sin, tana fatan yin kokari tare da Sin da nufin inganta dangantakar abokantaka irin ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.

A yayin da yake kasar Thailand, mista Li ya kai ziyara a fadar sarki don nuna juyayi, a madadin gwamnatin kasar Sin da jama'ar kasar ya nuna girmamawa ga sarki Bhumibol. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China