in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da babban taron tunawa da cika shekaru 80 da nasarar doguwar tafiyar sojin Sin
2016-10-21 15:21:53 cri

A yau Jumma'a ne aka kaddamar da babban taron tunawa da cika shekaru 80, da nasarar doguwar tafiyar da sojojin kasar Sin suka yi a nan birnin Beijing, inda babban sakataren jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin aikin sojin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da wani jawabi, yana mai jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da yada tunanin doguwar tafiyar domin kara ciyar da kasar ta Sin gaba.

Shugabannin JKS da na gwamnatin kasar, da wakilan sojojin da suka shiga doguwar tafiyar, da wakilan jama'a da suka zo daga bangarori daban daban, da wakilan sojojin kwatar 'yancin kasar Sin sama da dubu 3 ne suka halarci babban taron da aka shirya.

Bana shekara ce ta cika shekaru 80 tun bayan nasarar kammala doguwar tafiyar ta sojin kasar Sin, a saboda haka aka shirya bukukuwa iri iri a wurare daban daban a dukkanin fadin kasar, domin tunawa da wannan nasara. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China