Mahalarta taron a wannan karo sun kasance mafi yawa tun shekaru 43 da aka kulla yarjejeniyar, inda wakilai kimanin dubu 3 daga kasashe da yankuna fiye da 170 da hukumomin kasa da kasa fiye da 200 suke halartar taron wadanda kuma a tsawon kwanaki goma sha biyu za a tattauna batutuwa kimanin 120, da suka shafi batun kayyade cinikin dabbobin daji da tsire-tsire dake bakin karewa, kafa dokoki da gudanar da ayyuka bisa dokoki, tsara manufofin raya wannan fanni da dai sauransu.
Gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar wakilai daga hukumomi da kungiyoyin da abin ya shafa don halartar taron, kuma shugaban tawagar shi ne mataimakin shugaban hukumar kula da harkar daji ta kasar Sin Liu Dongsheng. (Zainab)