Kakakin MDD Stephane Dejarric wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce MDD ta yi kiyasin cewa, akwai mutane sama da miliyan guda da ke matukar bukatar agajin abinci a yankin na tafkin Chadi sakamakon rikicin Boko Haram.
WFP ya ce yana bakatar a kalla dala miliyan 72 nan da watanni 6 masu zuwa domin ya ci gaba da gudanar da ayyukansa na samar da abinci da sauran abubuwa masu gina jiki ga mutanen da suka bar muhallansu da ma masu daukar bakuncinsu.
Bayanai na nuna cewa, yankin tafkin Chadi dai ya kunshi kasashen Chadi da wani bangare mai girma na Jamhuriyar Nijar kuma yana daga cikin yankunan tafkuna masu girma a nahiyar Afirka. Kuma bai yi iyaka da kowane teku ba. (Ibrahim Yaya)