Tawagar tabbatar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Congo (MONUSCO) ta shaida a ranar Labara a birnin Kinshasa, kasancewar 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu kimanin dubu 20 a gabashin jamhuriyar demokuradiyyar Congo DRC, musammun ma a tsofuwar gundumar Orientale, inda wasu daga cikinsu dakaru ne masu dauke da makamai na reshen kungiyar tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar, in ji Felix Prosper, kakakin tawagar MONUSCO, a yayin wani taron manema labarai. (Maman Ada)