in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tura sabbin jiragen ruwa don yakar masu fashin teku
2016-08-18 09:57:30 cri

A jiya Laraba, gwamnatin Najeriya ta tura kananan jiragen ruwa kirar cikin gida kimanin 39 da wasu motocin aiki kimanin 45 domin ci gaba da farautar masu fashin teku.

Ministan tsaron Najeriya Mohammad Dan-Ali, ya ce, sojojin ruwan Najeriya ne suka kera jiragen, kuma an makala makamai a jikin jiragen, da kuma na'urorin dake baiwa jiragen kariya domin su gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Ya ce, wadannan jiragen 30 masu girma mita 8 da digo biyu, an kera su ne a cibiyar samar da kananan jiragen ruwa ta kasar dake kudancin birnin Fatakwal, za'a yi mafani da su wajen ci gaba da ayyukan sintiri a yankin Niger Delta, sannan akwai karin wasu guda 20 da za'a tura zuwa yankin sannu a hankali.

Da yake karin haske game da wannan batu, hafsan sojin ruwan Najeriya Vice Adimiral Ibok Ete-Ibas, ya ce, babu tantama wadannan jirage za su yi matukar amfani wajen taimakawa ayyukan jami'an na yaki da masu fashin tekun.

Ete-Ibas ya ce, rundunar sojin ruwan kasar ta yanke shawarar kera jiragen ruwa kimanin 60, a wani mataki na samar da isassun kayayyakin aiki ga jami'an tsaron ruwa na kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China