in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama shugaban kwamitin IOC na Turai a Brazil
2016-08-18 09:31:38 cri

Rahotanni daga Brazil na nuna cewa, an kama Patrick Hickey, mamba a kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, bisa zargin badakalar sayar da tikitin shiga gasar.

Hickey mai shekaru 71, shi ne kuma shugaban majalisar wasannin Olympics na Jamhuriyar Ireland, kana shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na Turai. Yana kuma aiki da hukumar zartaswar kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ne tun shekarar 2012.

An garzaya da Hickey zuwa asibiti, bayan da 'yan sanda a Brazil suka kewaye otel din da ya sauka, a wani bangare na binciken da ake yi masa game da cuwa-cuwar sayar da tikitin shiga gasar wasannin Olympics da ke gudana yanzu haka a birnin Rio na kasar ta Brazil.

Kakakin kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Mark Adams ya tabbatarwa manema labarai batun kamawa da kuma kwantar da Mr Hickey a asibiti.

Sai dai bai yi wani karin haske ba. Amma ya ce suna jiran matakin shari'a da mahukuntan Brazil din za su dauka kan Hickey.

Rundunar 'yan sandan birnin Rio dai ta ce, ana dai zargin Hickey da a kalla mutane 6 ne da sayar da tikitin shiga gasar ta Rio ta barauniyar hanya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China