in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A yau ne za a bude gasar wasannin Olympics na Rio a kasar Brazil
2016-08-05 14:55:26 cri

A yau Jumma'a da dare ne agogon kasar Brazil, za a kaddamar da bikin bude gasar wasannin Olympics na shekarar 2016 a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil. Tambayar a nan ita ce, wane irin biki mai kayatarwa a wannan karo birnin Rio de Janeiro zai nunawa duniya? A yayin wani taron manema labaru da aka shirya a jiya Alhamis, direktocin da suke shirya bikin bude gasar sun bayyana cewa, ko da yake sun fuskanci matsalolin rashin isashen kasafin kudi da na siyasa, amma duk da haka za a bude gasar wasannin Olympics na Rio ta hanyar nuna sigar Brazil, inda za a nuna wa duniya wani biki na musamman. Ga rahoton da abokin aikinmu Sanusi ya hada mana.

Da misalin karfe 8 na daren yau agogon kasar Brazil, za a kaddamar da bikin bude gasar wasannin Olympics na Rio na shekarar 2016. A cikin shekaru 7 da suka gabata, kungiyar direktocin shirya bikin kaddamarwa da kuma rufe gasar ta gamu da wahalhalu da dama sakamakon rashin isashen kasafin kudi.

A farkon soma shirya gasar wasannin Olympics na Rio, yawan kasafin kudin da aka kebe wa kungiyar direktocin tsara bukukuwan kaddamarwa da kuma rufe gasar ya kai dolar Amurka miliyan 110. Sabo da haka, kungiyar direktoci suka tsara wasu shirye-shirye masu jawo hankulan mutane sosai. Amma sakamakon koma bayan tattalin arzikin kasar Brazil a cikin 'yan shekarun nan, sannu a hankali aka rage yawan kasafin kudin zuwa rabin kudin da aka alkawarta kebe wa kungiyar, kuma an tsara yawancin kasafin kudi ne wajen samar da tsaro. A saboda haka, babu wani zabin da za a rage wa kungiyar, face ta yi watsi da fatan dake cikin zukatunsu, dole ne ta tsara shirye-shirye bisa hakikanin halin da ake ciki. Mr. Marco Balich, mai sa-ido kan yadda ake shirya bukukuwan kaddamarwa da kuma rufe gasar wasannin Olympics na Rio ya bayyana cewa, "A sakamakon matsalar rashin isashen kasafin kudi, ba za mu iya cimma burinmu na bayyana wa 'yan kallo shirye-shirye wadanda suke kunshe da sabon tunani. Bisa hakikanin halin da muke ciki yanzu, idan muka nunawa duniya wani kasaitaccen biki, wannan ba zai dace da halin da kasar Brazil take ciki ba. A ganina, abin da ya fi muhimmanci shi ne nuna wa al'ummar duniya kaunarmu da fatan dake cikin zukatanmu a zihiri."

Ban da matsalar karancin kasafin kudi, a 'yan watannin da suka gabata, an samu rikicin siyasa a kasar Brazil. Game da wannan magana, Mr. Marco Balich ya ce, siyasa ba ta taba zama ruhun wasannin Olympics ba. Ya kara da cewa, "Dalilin da ya sa ake takaita bukukuwan wasanin Olympics shi ne, ba domin wane ne yake kan mukamin shugabancin kasa ba. Alal misali, a yayin taron wasanin Olympics na Barcelona na shekarar 1992, za a iya tunawa da lokacin da aka harba kibiya wajen kunna fitilar gasar. Kuma a yayin wasanin Olympics na Atlanta na shekarar 1996, za a iya tunawa da Mohammed Ali, gwarzon dan dambe wanda ya kunna fitilar gasar duk da cutar kyarma da yake fama da ita a wancan lokaci. Wannan shi ne ruhun bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics."

Bayan wuya, aka ce sai dadi. Kungiyar direktocin shirya bukukuwan kaddamarwa da kuma rufe gasar wasannanin Olympics na Rio za ta yi maraba da wannan bikin da hanya maras sarkakiya. Mr. Fernando Meirelles, wato direktan da ya shirya fim din nan mai suna "The City of God" kana jagoran shirya bikin kaddamar da gasar ya ce, "Wani muhimmin tunanin da muke son mika wa duniya a yayin bikin kaddamar da gasar wasannin Olympics na Rio shi ne hakuri. A duniyarmu ta yau dake cike da rikice-rikice, hakuri abu ne mai muhimmanci matuka. Bugu da kari, muna son bayyana wa duniya fatanmu na kare muhalli a doron duniyarmu, da kuma inda muke zaune."

A wannan lokacin zafi na shekarar 2016, za a bude gasar wasannin Olympics karo na 31 a Rio de Janeiro bisa salo irin na Brazil, inda za a mika kauna da fatan alheri ga daukacin al'ummar duniya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China