in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a birnin Beijing
2016-07-28 16:50:04 cri

A yau Alhamis ne, aka bude bikin wake-wake da raye-raye na matasan kasashen Asiya da Afirka karo na farko a birnin Beijing, inda matasa 600 a bangarorin siyasa, kafofin watsa labaru, kasuwanci, nazari daga kasashen Asiya da Afirka 36 suka zo nan kasar Sin don halartar bikin.

Ana saran za su yi mu'amala da kara fahimtar juna ta hanyar bukukuwan da za a gudanar a tsawon kwanaki masu zuwa.

A cikin jawabinsa na bude bikin, Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya bayyana cewa, yana fatan matasan Asiya da Afirka za su tsaya tsayin daka kan tunanin cimma buri iri daya, da kokarin raya sabuwar dangantakar dake tsakanin kasashen duniya ta yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, ta haka ne za a tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa da amfanawa jama'ar kasashen Asiya da Afirka gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China