in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayyukan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika za su karfafa dunkulewar nahiyar Afrika
2016-06-23 11:03:49 cri

A yayin da Afrika take zaman jiran dunkulewar nahiyarta, gwamnatin kasar Sin ta sanar da tsare tsarenta na kafa manyan ayyukan da za su taimakawa nahiyar cimma burinta na dunkulewa.

A shekarar da ta gabata, gwamnatin Sin ta sanar da kaddamar da tsare tsaren ayyuka goma na hadin gwiwa da za su karfafa dangantaka tare da Afrika a cikin shekaru uku masu zuwa.

Tsare tsaren sun shafi fannoni zamanintar da noma, ababen more rayuwa, bunkasa masana'antu, harkokin kudi, taimako ga kasuwanci da zuba jari, kare muhalli, zaman lafiya da tsaro, rage kangin talauci da kyautatuwar jin dadin al'umma, kiwon lafiya da musanyar al'ummomi.

Haka kuma, kasar Sin za ta shawarta samar da dalar Amurka biliyan 60 domin tabbatar da aiwatar shirye shiryen ayyukan dangantaka.

Ministan kudi da tsara tattalin arzikin kasar Rwanda, Claver Gatete, ya bayyana a ranar Talata cewa, manyan gyare gyaren tattalin arzikin kasar Sin tare da Afrika za su taka muhimmiyar rawa wajen karfafa dunkulewar tattalin arziki a nahiyar.

Wadannan ayyukan tattalin arziki da sauran wasu kokari dangane da dunkulewar shiyyar ya rataya kan alkawarin karfafa kasuwanci tsakanin yankuna da kyautata makomar zuba jari a nahiyar, da ma kuma takara tsakanin 'yan Afrika, in ji mista Gatete.

Dunkulewar kasuwancin Afrika ya kasance tun da jimawa wani babban burin masu fada a ji a siyasa da masanan tattalin arzkin Afrika.

A ranar 10 ga watan Yunin shekarar 2015 a birnin Alkahira, yankin musanya cikin 'yanci na bangarori uku (ZLET), an kaddamar da shi domin ingiza ci gaban tattalin arzikin Afrika.

Yankin ZLET ya kunshi manyan yankunan tattalin arzikin Afrika uku, da suka hada gamayyar ci gaban kudancin Afrika (SADC), gamayyar gabashin kasashen Afrika (EAC), da kuma yankin kasuwancin hadin gwiwa na arewacin Afrika da kudanci (COMESA).

Tun a shekarar 2000, kasar Sin ta kara tallafinta, da kuma gudanar da ayyukan dangantaka tare da kasashen Afrika ta hanyar dandalin dangantaka na Sin da Afrika (FOCAC).

FOCAC, ya kasance wani tsarin shawarwari da tuntubar juna na hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma tun lokacin kaddamar da shi, gwamnatin Sin ta zuba biliyoyin dalar Amurka ga kasashen Afrika domin ci gaban tattalin arzkinsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China