Tawagar ta Quartet ta kunshi jami'an diplomasiyya da suka hada da na MDD da kungiyar tarayyar Turai EU da na kasashen Rasha da Amurka, wadanda ke samun goyon bayan sauran kasashen duniya domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da al'ummar Palastinawa.
Quartet, ta nanata cewar, akwai bukatar kasashen duniya su ba da gudumawarsu a kokarin da ake na samar da kyakkyawan yanayi wanda zai tabbatar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.
Wannan sanarwa ta zo ne, bayan wata ganawa tsakanin babban sakataren MDD Ban Ki Moon da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da kuma wakilin EU Federica Mogherini, kuma sun yi ganawar ne a lokacin babban taron MDD. (Ahmad Fagam)