A Birtaniya mutane kimanin 300 ne suka taru a kofar majalisar dokokin kasar a jiya Asabar domin nuna rashin jin dadi kan sakamakon zaben raba gardama kan batun ficewar kasar ta Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai wato EU, inda suka yi kira da a sake yin zaben raba gardamar. A wannan rana kuma, babbar ministar gwamnatin Scotland Nicola Sturgeon ta nemi kungiyar EU da ta tattauna game da matsayin da yankin Scotland ke dauka a cikin kungiyar EU bayan da aka balle kasar Birtaniya daga kungiyar EU.(Lami)