in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An soma dudduba kan yadda hakkin bil Adama yake a kasar Sin
2013-10-23 18:18:33 cri

Jiya 22 ga wata a birnin Geneva ne aka tattauna kan yadda hakkin bil Adama yake a kasar Sin a yayin taro karo na 17 na kungiyar kare hakkin bil Adama ta MDD. Wannan ne karo na biyu da kungiyar ta MDD ta dudduba batun hakkin bil adama a kasar Sin.

Tawagar kasar Sin da ta shiga aikin tare da wakilan da suka fito daga hukumomi 17 na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, da gwamnatocin yankunan musamman na Hongkong da Macau. A cikin jawabin da ya yi a yayin taron, shugaban tawagar, kuma manzon musamman na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin mista Wu Hailong ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta karbi shawarwari guda 42 da gwamnatocin wasu kasashe suka gabatar a yayin da aka yi mata bahasin zagayen farko a kan wannan batu yau shekaru hudu da suka gabata, ta kuma yi alkawarin cewa, "a yayin da aka kara duba wannan batu, kasa da kasa za su gano wata kasar ta Sin da ta kara samun ci gaban tattalin arziki, kyautattuwar dimokuradiya tare da tsarin dokoki da shari'a, daidaituwar zaman al'umma, da jin dadin zaman jama'a." A yanzu dai Sin ta kara kawo gyara a wannan fanni, ana iya cewa, kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi a lokaci na kara kyautata hakkin bil Adam a kasarta. Mista Wu yana mai cewa,

"A yau bayan shekaru hudu, ina son gaya maku a nan cewa, mun riga mun tabbatar da wasu shawarwarin, wasu kuma muna ci gaba da gudanar da su, ana iya cewa, kasar Sin ta cika alkawarinta. Bayan shigar da abubuwan da suka shafi batun inganta hakkin bil Adama da kare hakkin bil Adama cikin tsarin mulkin kasar Sin da tsarin jam'iyyar Kwaminis ta kasar, gwamnatin kasar ta Sin ta gama aikin aiwatar da shirin ayyukan hakkin bil Adama na kasar na shekarar 2009 zuwa 2010 cikin lokacin da aka tsai da, har ma a watan Yuni na shekarar 2012 ta tsara da kuma kaddamar da shirin na shekarar 2012 zuwa 2015."

Mista Wu ya kara bayyana cewa, a shekaru hudu da suka gabata, kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan kyautata zaman rayuwar jama'a, inganta harkar samun guraban aikin yi, kana ta mai da batun kare ikon rayuwa da na samun ci gaban jama'arta a gaban kome. Wu ya ce,

"Tabbatar da hakkin bil Adama a hakika na bukatar samun tabbaci wajen aiwatar da dokoki. Ta hanyar kaddamar da shirin dokoki, da shirya tarurrukan saurarar ra'ayoyi, da na tattaunawa, da dai sauransu ne, kasar Sin ta ingiza jama'arta shiga aikin dokoki. Hakan dai jama'ar kasar sun kara samun tabbaci a fannin ikonsu ta fuskar siyasa. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar ta Sin ta yi ta kokarin karfafa tsarin dokokin shari'a, tare kuma da mai da batun kare hakkin bil Adama a matsayin muhimmin aikinta."

A yayin taron kuma, wakilai na kasashe 137 sun yi jawabi da kuma gabatar da shawarwari kan yadda hakkin bil Adama yake a Sin, tawagar Sin ma ta amsa tambayoyin da suka gabatar. Yawancin kasashe sun nuna tabbaci sosai kan babban ci-gaban da Sin ta samu ta fuskokin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, tsare-tsaren dimokuradiyya da dokoki, kare ikon rukunonin mutane na musamman, hadin gwiwar dake tsakanin kasar da kasa da kasa a fannin hakkin bil Adama, da sauran batutuwa. Zaunanniyar wakiliyar kasar Cuba dake Geneva a cikin jawabinta ta nuna yabo sosai kan nasarar da Sin ta samu kan inganta da kare hakkin bil Adama:

"Kasar Sin ta gudanar sosai da shawarwarin da aka gabatar mata a yayin duba rahoton zagayen farko tare da samun babbar nasara. Gaskiya kasar Sin tana kokarin inganta da kyautata yanayin hakkin bil Adama nata. Akwai bukatar mu jaddada a nan cewa, kasar Sin ta tsara shirin ayyukan kare hakkin bil Adama, kana kuma ta samu ci gaba a fannin ba da tabbaci kan zamantakewar al'umma."

A nasa bangaren ma, mista Abdul Samad Minty, zaunannen wakilin kasar Afrika ta Kudu dake Geneva, ya nuna yabo ga dauwamammen ci gaban tattalin arziki da Sin ta samu a shekaru hudu da suka gabata, tare kuma da tabbatar da nasarorin da ta samu wajen cimma muradun karni na MDD, girmama ikon samun ilmi da rayuwar jama'a, da dai sauransu. A sa'i guda, yana fatan amfana da fasahohin da Sin ta samu, da kuma hanyar da take bi wajen kare ikon samun bunkasuwa da na rayuwa:

"Hakkin bil Adama na iya kawo tasiri ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Muna fatan ba kawai kasar Sin ta kyautata yanayin hakkin bil Adama nata kawai ba, har ma za ta iya taimakawa sauran kasashe, ciki har da kasashen Afrika. Kasar Sin ta riga ta ba da taimako ga kasashen Afrika wajen hakkin bil Adama, wannan abu ne mai kyau sosai, irin wannan hadin gwiwa ya taimaka wa kasashen Afrika wajen samu ci gaba a fannin."

Game da shawarwarin da wasu kasashen yamma suka gabatar kan batutuwan da suka shafi yin kwaskwarima kan tsarin dokoki, da ayyukan kungiyoyin da ba na gwamnati ba, da kuma hada kai da tsarin hakkin bil Adama na MDD, mista Wu ya nuna cewa, har yanzu ma kasar Sin na fuskantar matsaloli da kalubale da dama, saboda haka tana son karfafa yin mu'amala da hadin kai tare da kasashen duniya. Kasar Sin ma na son yin la'akari da shawarwarin da suka dace, kuma za ta yi nazari da tabbatar da su bisa yanayin da kasar ke ciki. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China