in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin cinikin Alibaba na bana ya zarce yuan triliyan 3
2016-03-22 11:13:06 cri

Rukunin Alibaba a ranar Litinin ya sanar da cewar, adadin kudin cinikinsa bisa tsarin kasafin kudi na shekarar 2016 har ya wuce da RMB yuan triliyan 3 wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 463.

Tsarin kasafin kudi na shekarar 2016 na kamfanin Alibaba ya tashi daga ran 1 ga watan Afrilun shekara ta 2015 zuwa 31 ga watan Maris na wannan shekarar.

Alibaba ya ce, zai iya wuce na rukunin Wal-Mart a wannan shekarar ta 2016, ya zama kafar sarin kayayyaki mafi girma a duniya.

Kayayyakin amfanin gida, tufafi, na'urorin lantarki, da kayayyakin jarirai na daga cikin nau'in kayayyakin da suka fi samun karbuwa a kafar ciniki ta Alibaba, in ji kamfanin.

Mata ne kuma suke da rinjaye wajen amfani da kafar da suka kai adadin fiye da rabin masu amfani da kafar sayyaya ta Taobao, sannan kuma matasa su ne mafi yawan masu sayayyar, in ji Alibaba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China